Gwamnonin shiyar Arewa masau gabas sun lashi takwabin gudanar da aiyukan cigaban yankin.

Gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun baiyana bukatar hadin kan yankin, yayin da kungiyar gwamnonin na arewa maso gabas ta yanke shawarar aiki tare da kamfanin wutan lantarki na Shanghai domin gina cibiyar wutan lantarki mai amfani da coal da zai bada wuta mai karfin megawatt sittin , ko mai amfani da karfin rana da zai bada wuta mai karfin megawatt hamsin domin shawo kan matsalar wutan lantarki a yankin. Daukan wannan maataki na kunshe ne cikin jerin matakan da kungiyar gwamnonin ta dauka a kaeshen zaman ta karo na tara da tayi a birnin Yola, fadar jahar Adamawa. Wadannan matakai wanda gwamnan jahar yobe , Mai Mala Buni ya karanto a madadin takwarorin shin a yankin yace , sun cin ma matsayar cewa ko wace jaha ta dau wannan batu na hadin kai da muhimmanci, ta hanyar daura hakkin tabbatar da hakan a wuyan babban jami’i. Yayin da ta baiyana sauyin yanayi da gurbacewar muhalli a matsayin wasu manyan batutuwa da suka addabi yankin, gwamna Mai Mala Buni yace kungiyar ta yanke shawarar shiga kawance da duk wani shiri yakar hakan kamar Great Green Wall da dai sauran su. A cewar gwamnan, kungiyar tayi na’am da shirin gwamnatin jahar Bauchi na daukan nauyin taron baza koli tsakanin ranar 26 na watan fabrairu zuwa uku ga watan maris na 2024, tare da kira ga mazauna yankin da su halacci wannan baza koli, ta kuma gaiyaci kasa, nahiyar afrika da ma duniya baki daya da su zo domin gane wa kan su irin damammakin tattalin arziki da ke yankin. Kungiyar ta kirayi jahohi da basu aiwatar da dokar ilimi na 2022 ba , kamar yadda majalisar ilimi na arewa maso gabas ta bada shawara a taron ta karo na takwas, da su gaggauta yin hakan domin hade kan yankin. Gwamna Buni yace ana samu kyakkyawar sauyin lamarin tsaro a yankin, kuma kungiyar ta bukaci Karin kawance da juna gurin tsarin tsaron yankin, da kuma aiki tare da cibiyoyin tsaro domin bullo da tsarin tsaro na bai daya a yankin arewa maso gabas. Yace, kunigiyar ta yi hange a fannin ci gaban tattalin arzikin yankin, ta kuma yanke shawarar yin aiki a matsayin tsinstsiya madaurin ki daya gurin karfafa ci gaban al’umma da na mu’amala tsakanin juna. Yayin da ta nuna damuwarta kan yanayin manyan hanyouin gwamnatin taraiya dake tsakanin jahohin wadanda akayi watsi da su, kungiyar ta yi kira ga ma’aikatar aiyuka na taraiya da bi sawun kwangilolin manyan hanyoyi da aka bayar a yankin arewa maso gabas, tare da kokawar cewa rashin kyawun hanyoyin wani babban dalili ne na matsalar tsaro, wanda yake tsaida harkokin ci gaba, tare da jefa al’umma cikin mawuyacin hali a yankin. Gwamnan yace, kungiyar har way au ta yanke shawarar kira wa hukumar ci gaban yankin arewa masu gabas da tayi aiki tare da gwamnatocin jahohi da ma’aikatar aiyuka na taraiya domin kau da matsalolin da suke tattare a cikin kwangilolin aiyukan manyan hanyoyi, wanda suke kawo tsaiko gurin ci gaba, tare da bullo da hanyoyi da zasu taimaka. Yace, kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta kan tsarin layin dogo a yankin, wanda ke bukatar zamanantarwa, da wannan ne ta mika bukatar saka yankin cikin tsarin hukumar zirga zirgan jirgin kasa ta kasa domin itama a saka ta cikin tsarin layin dogo na zamani, wanda yankin ta rasa. Gwamna Buni ya kuma kara da cewa, kungiyar ta yanke shawarar gudanar da taron ta karo na goma a jahar Bauchi tsakanin ranar 23 ga watan fabrairu zuwa 26 ga watan maris na 2024.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE