Hukumar NDIC ta shiryawa dalube taron fadakarwa dangane da ajiya a Bankuna a jahar Adamawa.

Daga Ibrahim Abubakar.
A yayinda aka gudanar da ranan Adana ta duniya hukumar inshoran Bankuna a Najeriya wato NDIC ta shirya taron wayarwa daluben makarantar gaba da firamare a kalla 100 kai dangane da yadda zasu kasance suna ajiyar kudinsu domin inganta rayuwarsu. Da yake jawabi a wurin taron ko odinatan hukumar a shiyar yola Victor Egba yace makasudin shiryawa daluben wannan taron dai shine wayarwa daluben kai dangane da muhimmanci ajiya a banki wanda hakan zai tamaka musu wajen tafiyar da rayuwarsa yadda ya kamata. Wakilin Al Nur ya rawaito cewa a ranan 31 ga watan oktoba ne dai ake gudanar da bikin ranan adana ta duniya domin nuna irin muhimmanci ajiya ke dashi. Egba ya kara da cewa aniyar hukumar dai itace fadakar da daluben yadda zasu kasance suna ajiyar kudinsu a bankuna domin kare martabarsu. Domin yana daya daga cikin manufofin hukumar ta NDIC ta kare masu ajiya a Bankuna domin basuyi asaran kudadensuba. Acwarsa kafin yanzu da zaran banki ta durkushe to masu ajiya a bankinma sunyi asara amman a yanzu lamarin ba haka yakeba domin hukumar ta tsaya kai da fata domin kare masu ajiya a asusunsu na banki. Shima a jawabinsa kwamishinan ilimi a jahar Adamawa Alhaji Garba Pella godiya yayiwa hukumar ta NDIC bisa shirya wannan fadakarwa da tayiwa daluben tare da shawartan daluben da suyi amfani da abinda aka fadakar dasu domin samun nasara. Kwamishina wanda darektan gudanarwa maikatar ilimi jahar Simnawa Geoffrey ya wakilta ya baiyan cewa wanan fadakarwa da akayiwa daluben babban nasarace domin zai taimakawa matasa. Itama mataimakiyar darektan hukumar a Abuja Mis Ragina Dimlong inda ta gabatar da jawabi kan aiyukan hukumar ta NDIC tace gwamnatin tarayya ta samar da hukumar ne domin kare dukkanin masu ajiya a bankuna domin ganin kudadensu basu salwantaba. Ta kara da cewa hukumar tana hada kai da Babban Bankin Najeriya CBN domin lura da dukkanin bankuna domin ganin sun gudanarwa kwastomominsu aiyuka da suka kamata. Ta kuma baiyana cewa hukumar tana kare masu ajiya ne Amman bata hurda da kwastomomi kai tsaye suna laakari da gazawar bankunanne.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE