Hukumar raya yankin arewa masau gabas ta gamsu da yadda aiyukan ke tafiya a yankin na arewa masau gabas.

Sabbin nadaddun mambobin hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas, wato NEDC sun kai ziyarar ban girma a fadar mai martaba lamidon Adamawa. Shugaban hukumar, Manjo Janar Paul Tarfa ma I ritaya yace a kwai bukatar ziyaran yankin, a kuma gana da masu ruwa da tsaki da kuma gabatar da mambobin hukumar tare da Karin hasken nasarori da hukumar da cin ma. Shugaban hukumar ya kara da cewa sun zo jahar Adamawa ne domin duba wasu aiyuka da akeyi a jahar, su kuma san inda aka dosa domin gi gaban hukumar. Ya yaba da kokarin mai martaba Lamidon Adamawa na tabbatar da zaman lafiya tare da mika bukatan addu’oi da shawarwari domin ci gaban hukumar da ma yankin are maso gabashin Najeriya baki daya. Da yayi jawabi, mai martaba Lamidon Adamawa, dakta Barkindo Aliy Mustafa wanda Galadiman Adamawa, Mustafa Aminu ya wakilta yayin ziyaran ya yi na’am da ziyaran mambobin hukumar, wanda ya baiyana a matsayin karramara masarautan baki daya. Ya kuma taya manjo janar Tarfa mai ritaya murnan sake kasancewa shugaban hukumar, da kuma dau alwashin cewa mu’amala dake tsakanin hukumar da masarautan zata ci gaba da kara karfi domin ci gaban jahar dama yankin baki daya. A wani makamancin haka kuma, hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas, NEDC ta baiyana gamsuwar ta da yadda aiyukan da ta bayar a yankin ke tafiya. Shugaban hukuar ta NEDC, manjo janar Paul Tarfa mai ritaya ne ya baiyana haka yayin da yake amsa tamboyi daga manema labaru bayan ya zagaya ya duba aikin ginin makarantan sakandaren zami wato Mega Secondary school a karamar humar song na jahar Adamawa. Manjo Janar Paul Tarfa mai ritaya ya baiyana gamsuwar shi da yadda aiyukan ke gudana, tare da fatan sauran aiyukan ma za a gudanar da su cikin nasara kamar haka. Hukumar ci gaban yankin arewa masu gabas tace zata gina irin wadannan makarantu guda goma sha takwas a yankin , inda jahar Adamawa zata samu uku. Mambobin hukumar za su zaga yankin ne domin duba aiyuka da ake yi da kuma yin gyara a duk inda ya kamata domin tabbatar da cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Wasu daga cikin aiyukan da aka duba sun hada da na aikin ginin makarantan sakandare a karamar hukar girei, da aikin gyare gyare na makarantan koyan sana’aoi daje garin Jibiri na karamar hukumar girei da kuma aikin ginin sashin maraba da baki wato accident and emergency dake asibitin koyarwa na Modibbo Adama dake yola.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE