Jam iyar NNPP dake jahar Taraba tace ta kimtsa tsaf domin shiga adama da ita a zabukan kananan hukumomi dake fadin jahar.

Daga Sani Yarima Jalingo
A yayinda ake daf da gudanar da zabuka a dukkanin kananan hukumomi jahar Taraba Jam Iyar NNPP a jahar Taraba ta kammala dukkanin shirye shirye da suka kamata domin tunkaran zaben dake tafe a jahar . Shugaban Jam Iyar NNPP a jahar Taraba Alhaji Abdullahi Ade ne ya baiyana haka a lokacinda yake amsa tambayoyin Yan Jarida a ofishinsa dake Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba. Ya dukkanin shirye shirye da suka kanata da suka hada da yin katin shaidar wakilainsu na runfunan zabe wato Tags duk suyisu. A cewarsa dai kawo yanzu suna da Yan takaran shuwagabanin kanana hukumomi shida da suka hada da Jalingo, Ibi, Yerro, Karim lamido, Gassol, da Kuma Sardauna. Dangane da Yan takaran kansiloli kuwa sai shugaban ya baiyana cewa suna da Yan takaran kansiloli akalla 40 wadanda suka tsaya takara a kananan hukumomi sha shida dake fadin jahar. Da yake tsokaci dangane da matakin da Jam Iyar UPP ta dauka na marawa Jam Iyar PDP baya a zaben sai Hon Abdullahi yace jam iyatsu ta NNPP bata cikin irin wannan yarjejeniya saboda itama zata shiga a dama da ita a zabukan kananan hukumomin. Saboda haka bama tare da Jam Iyar ta UPP Kuma bama kalubalantar matakin da ta dauka saboda tana da yancin yin haka na marawa duk Wanda takeso baya. In Kun lura wadannan sune katunan shaidar wakilain mu ne saboda haka bamujanyeba daga shiga zaben Kuma da yardan Allah zamuyi nasara. Zan sake nanatawa dangane da jawabinda shugaban hukumar zaben jahar Taraba Dr Danladi Phillip Duwe ya tabbatar mana da cewa za a gudanar da zabe Mai inganci don haka akwai alaman yin adalci a zaben. Saboda shugaban hukumar zaben dattijone Wanda yake da shekaru Sama da 70 Wanda bazai amince dayin ba daidaiba. Shugaban Jam Iyar ta NNPP Hon.Abdullahi Ade ya kirayi dukkanin magoya bayansu da fito kansu da kwarkatarsu a ranan zabe su zabi Yan takaransu tare da shawartarsu a matsayin na yan jahar sukasance masu bin doka doka da oda domin Samar da zaman lafiya dama saamun nasaran gudanar da zabe na ran 18-11-23 lafiya a fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE