Jam iyar NNPP a jahar Taraba ta baiyana aniyarta shigaba zabukan kananan hukumomi a fadin jahar.
Daga Sani Yarima Jalingo
A yayinda zaben kananan hukumomi ke karatowa. Shugaban jam iyar NNPP a jahar Taraba Hon. Abdullahi Ade ya jadda cewa zaben kananan hukumomin zai gudana cikin inganci.
Ade ya baiyana hakane a lokacinda yake yiwa manema labarai jawabi a Jalingo Fadar gwamnatin jahar ta Taraba.
Yace jam iayarsu ta NNPP ta amince zata shiga a dama da ita acikin zaben kananan hukumomi duba da yadda shugaban hukumar zaben jahar Taraba wato TSIEC Dr Danladi Phillip Duwe ya tabbatar da cewa dukkanin jam iyun siyasa jahar suna da daman shiga zaben kuma za a gudanar da zabe mai inganci.
Ya ce mun gudanar da taro da shugaban hukumar zaben na jahar Taraba Dr Danladi biyo bayan gayyatanmu da yayi bayan an fitar da jadawalin zaben kananan hukumomi kuma muyi taro akalla ya kai sau biyar tare da yi mana alkawarin cewa hukumar zata gudanar da karbabben zaben a fadin jahar.
Acewar shugaban jam iyar ta NNPP dai ya baiyana shugaban hukumar zaben a matsayin jajircecen mutunne wajen shirya zabukan kananan hukumomi don ko a zamanin gwamna Darius Ishaku hukumar ta gudanar da zabe mai inganci tare da adallaci. Kuma yana da yakinin wannan gwamana maici a yanzu wato Agbu Kefas zai sakewa hukumar mara domin ta gudanar da zaben da zai karbu ga jama a. Ba tare da tada jijiyoyin wuyaba.
Shugaban Jam iyar yace akullum yana bada misali da jahar Kaduna a lokacinda El Rufai yana gwamna inda jam iyar PDP ta samu nasaran cin kujerun kansila dana shuwagabannin kananan hukumomi musammanma kudancin Kaduna, ko a jahar neja ma an samu irin wannan.
Yace in har jam iyar mai ci zatayi magudin zabe ta baya tunanin cewa jam iyun adawa sasu kasance suna shiga zabe domin ba dimokiradiya akeyiba.
Alhaji Abdullahi ya kirayi dukkanin magoya bayan jam iyar ta NNPP da su fito kwansu da kwarkatarsu ranan 18-11-2023 domin zaben jam iyar NNPP kuma sukasance masubin doka da oda domin hukumar zabe tayi alkawarin kidiya kuri un zaben a runfunan zaben.
A cewarsa suna da yan takara shida na shuwagabanin kananan hukumomi Wanda suka hada da Jalingo, Karim lamido, Gassol, Yerro, Ibi, da kuma Sardauna. Kuma suna da yan takaran kansilolima a wasu kananan hukumomi.
Ya kuma baiyana gamsuwarsa da yadda hukumomin tsaro suka dauki matakin tsaro domin ganin an gudanar da zaben kananan hukumomin lafiya.
Comments
Post a Comment