Majalisar dokokin jahar Adamawa ta amanice da sunayen shuwagabanin gundumomin raya yankuna dake fadin jahar.
Majalisar dokokin jahar Adamawa ta amince da sunayen mutane hamsin na shuwagabanni gundumomin raya yankuna da sakatarorinsu a jahar Adamawa.
Amincewar ya biyo bayan wasikar bukatar amuncewa da sunayen da gwamna Ahmadu Umaru Finti ya akewa majalisar wanda kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Bathiya Wesley ya karanta a zauren majalisar a zamanta da tayi a ranan litinin.
Dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Maiha Ahmed Jingi Belel ne ya taso da batun amincewa da sunayen shuwagabanin gundumomin raya yankin da sakatarorinsu wanda ya samu goyon bayan memba mai wakiltar Verre Japhet Hammanjabu.
Daga nan sai kakakin majalisar Bathiya Wesley ya umurci akawun majalisar da ya gabatarwa majalisar zantarwar jahar batun amincewar domin daukan mataki na gaba.
Comments
Post a Comment