Makarantar NAFAN ta shiryawa daluben Firamare gasar wasanni a wani mataki na kara musu kwarin gwiwar wajen karatu.

A wani mataki na karawa yara kwarin gwiwa karatu domin su samu inganceccen ilimi hakan yasa makarantar NAFAN Academy ta shiryawa daluben makarantar firamare wasanni a tsakanin daluben makarantar. Wasannin da an dauki kwanaki biyar ana gudanarwa wanda kuma an gudanar da wasanni daban daban da suka hada da wasan tsare, fareti, tsalle, da dai sauransu. Bikin kammala wasannin dai ya samu halartan shugaban makarantar Alhaji Adamu Jingi wanda akafi sani da maihange tare da iyalensa dama shuwagabanin makarantar sakandare dana kwalejin kimiya kiwon lafiya, da kuma mataimakin short gaban kungiyar malamai ta kasa N U T shirya karamar hukumar yola ta arewa.
Da yake jawabi shgaban makarantar Alhaji Adamu Jingi ya baiyana godiyarsa dangane da shirya wannan gasa tare da kiran iyaye da su baiwa makarantar ta NAFAN hadin kai da goyon baya domin ganin makarantar ta comma burinta na baiwa yara nagarceccen ilimi domin gobenmu tayi kyau. Ya kuma yabawa malamain makarantar bisa jajircewa da sukeyi dama sadaukar da kai wajen karantar da daluben a koda yaushe wanda acewarsa suna taka rawan gani kuma abun a yabane. Ya kuma kirayi daluben da su kasance masuyiwa iyaye biyayya dama malamai wanda hakan zai basu damar samun ilimi mai albarka da kuma samun albarkar rayuwa a koda yaushe. Shima a jawabinsa mataimakin shugaban kungiyar Malamai wato NUT shiyar karamar hukumar yola ta arewa Muhammed Awal Yakub ya baiyana farin cikinsa da jin dadinsa dangane da shiryawa yaran wannan gasa wanda acewarsa hakan zaikarawa daluben kwarin gwiwa cigaba da karatunsu yadda ya kamata. Shima shugaban makarantar ta firamare Suleiman Ali Jakada godiya yayiwa wadanda suka halarci bikin tare da shawartan iyaye da su kara himma wajen turo yaransu makarantar akan lokaci domin a acewarsa hakan zaitaimaka wajen baiwa yara inganceccen ilimi.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE