Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani Mai shekaru hamsin da ake zargi da cin zarafin karamar yarinya.
A kokarinta na dakile aikata cin zarafin yaran mata a fadin jahar rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani mutum Mai shekaru 53 Mai Suna Usman Tela Ahmadu mazaunin samunaka dake cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa bisa zarginsa da yiwa wata yarinya Mai fama da tabin hankali fyade.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola.
Wanda ake zargi da ya fitone da Maiduguri dake jahar Borno inda yake zaune a wurin a matsayin dan gudun hijira wanda Kuma Yana samu taimako daga jama a.
Bincike ya nuna cewa Wanda ake zargin Yana cin zarafin yarinyar da take fama da tabin hankali tun daga shekara ta 2021.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana damuwarsa dangane da aukuwar lamarin tare da shawartan iyaye da sukasance suna maida hankali kan yaransu a Koda yaushe da Kuma taimakawa rundunan yan sandan da bayanai sirri domin kawar da irin wadan natagari a tsakanin Al umma.
Domin Babu mabuyar masu aikata laifuka a fadin jahar Adamawa saboda rundunan ta tsaya da kafanta domin ganin an samu zaman lafiya a fadin jahar baki Daya.
Comments
Post a Comment