Rundunan yan sandan jahar tana tsare da wani da ake zargi dayiwa yar shekaru biyar fyade.
Rundunan yan sandan jajar Adamawa a kokarinta na dakile cin zarafin yara yanzu haka tana tsare da wani wanda ake zargi da yiwa wata yarinya fyade a karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yam sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya naiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan tace rundunan ta samu koke da wani magidanci mai suna Adamu Ahmed mazaunin Dikon Nasarawa a karamar hukumar Mayo Belwa cewa anyiwa yarsa mai shekaru biyar fyade.
Daga jin wannan labari kwamishina yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola baiyi da wasaba. Tunin ya umurcin Jami an yan sandan dake Mayo Belwa da su gudanar da bincike kan lamarin domin tsare wanda ake zargi da aikata fyaden.
Bisa bincike da aka gudanar dai yanzu haka ana tsare da wani mai suna Musa Inusa mai shekaru talatin da ake zargi da yiwa yarinyar fyade .
Kuma ma bincike ya nuna cewa shi wanda ake zargin ya dade yana satan dabbobin gida a Nasarawo Dikon. Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan ya bada umurnin gabatar da wanda ake zargin kotu domin ya fuskanci sahri ya.
Comments
Post a Comment