Rundunan yan sandan Najeriya ta taimakawa magadan jami anta da suka mutu a bakin aiki.

Rundunan yan sandan Najeriya ta baiwa magadan jami an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a lokacinda suke gudanar da aiyukansu na kare Martaban kasa . Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ne ya kaddamar da bada cek din kudaden ga iyalen marigaya karkashin tsarin nan dake kula da walwalan Jami an yan sanda inda iyale 613 ne suka amfana da tallafin biyo bayan mutuwar yan uwansu a cikin shekaru da suka kama daga shekara ta 2020/2021 da 2021/2022 sai kuma 2022/2023. Da yake jawabin a wurin bikin tallafin da ya gudanar a shelkwatar rundunan yan sandan dake Abuja. Babban sifeton yan sandan ya baiyana irin muhimmanci da irin wannan taimako yake dashi domin rundunan ta kudiri aniyar kula da walwalan dukkanin Jami anta a koda yaushe kama daga wadanda suka rasa rayukansu a bakin aiki ko kuma wadanda sukati ritaya. Hakan na knshene a cikin wata sanarwa daga kakakin rundunan ta kasa ACP Olumuyiwa Adejobi a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. A sanarwan anjiyo Babban sifeton yan sandan na cewa yawan kudi da aka bayar sun kai nera bilyon biyu da milyon dari biyu da saba in da shida da dubu dari da goma da dari tara da sittin da shida da kobo sha takwas wato (2,276,110,966.18k).ya kuma kara da cewa wannan shine karo na uku ake gudanar da irin wannan taimako tunda ya fara aiki a matsayin Babban sifeton yan sandan tare da mika tazaiyarsa da alhininsa ga iyalen wadanda suka rasa rayukansu inda ya baiyanasu a matsayin wadanda suka sadaukar da Kansu wajen kare kasarsu tare da gabatar musu da cek din kudi ga kowanensu domin magadan su samu saukin rayuwa. Babban sifeton ya kuma baiyana cewa rundunan zataci gaba da yin aiki tukuru domin ganin an kula da hakkin Jami an yan sandan a koda yaushe domin ganin sun samu kwarin gwiwa cigaba da aiyukansu yadda ya kamata. Ya kuma yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa kokarinsa na tallafawa domin kula da walwalan Jami an yan sandan akan lokaci ta tsarin inshoran nan ta Premium.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.