Rundunan yan sandan Najeriya tana daf da rufe shafin diban jami an yan sanda.
Rundunan yan sandan Najeriya tace duk da cewa ana daf da rufe shafin yanan gizon diban Jami an yan sanda kawo yanzu runduna ta samu wadanda suke bukatar shiga aikin yan sandan sunkai dubu dari biyar da arba in da bakwai da dari bakwai da saba in da hudu.547,774. tunda aka bude shafin tun daga ranan 15-10-2023. Wanda kuma za arufe a ranan 26-11-2023.
Mr Ikechukwu Ani shine Jami in watsalabarai sashin diban Jami an yan sandan ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwan ta baiyana cewa cikin mutane 547774 wadanda suka bukaci shiga aikin yan sanda 358,900 ne suka samu nasaran shiga zagaye na farko biyo bayan gwaje gwaje da aka yi musu na kiwon lafiya da dai sauransu.
A yayinda 84,606 kuwa basu samu shigaba duba da matsaloli da aka samu da suka hada da yawan shekaru, saboda ana bukatar wadanda shekarunsu suka kama daga 18-25.
Kawo yanzu dai jahar Kaduna itace na farkon yawan wadanda suka bukaci Shiga aikin yan sanda da yawansu yakai 40,272 sai jahar Adamawa ke biye da mutane 36,398 a yayinda jahar Borno ta zo ta uku da mutane 31,122. jahar Benue itace ta hudu da mutane 32,048 sai jahar Katsna tazo ta biyar da mutane 30,202 jahar Bauchi ta shida da mutane 30,604 da Kano tazo na bakwai da mutane 30,004. Itama jahar Ebonyi tana da mutane 2132, jahar Lagos tana da mutane 2324, jahar Bayelsa tana da mutane 2651 jahar Abia tana 2796. jahar Anambara 1664.
Tsohon Babban sifeton yan sandan Najeriya Dr Solomon Arase ya baiyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da aiyukan diban yan sandan, domin baiwa matasan Najeriya damar bada tasu gudumawa wajen infanta tsaro a fadin Najeriya.
Ya kuma shawarcin matsan yankin kudancin Najeriya da suka shiga aikin yan sandan domin samun damar kakkabe matsalar tsaro a yankin.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar zatayi iya kokarinta domin ganin an gudanar da adalci a diban Jami an yan sandan.
Comments
Post a Comment