Wani jami in dan sanda ya rasa ransa sakamokon rikici a tsakanin sojoji da yan sanda a jahar Adamawa.

Kwamishina yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yayi Allah wadai da rikici da faru a tsakanin yan sandan da sojoji a Target Junction cikin karamar hukumar yola ta arewa biyo bayan musayan harbe harbe da sukayi a tsakaninsu lamarin da yayi sanadiyar mutuwar wani Jami in dan sanda mai mukamin isfeto. Kakakin runduna yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiayan haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Kwamishinan yan sandan tunin ya bada umurni da a gaggauta gudanar da bincike dangane da lamarin. Sanarwan ta kuma baiyana cewa kwamshina ya baiyana ta kaicinsa lamarin da yace abin takaicine ace ana samun irin wadannan hare hare a tsakanin hukumomin tsaro Jami an da suke gudanar da aiyukansu domin kare rayuka dama dukiyoyin al umma kuma sannan ace ana kai musu hari wannan ba daidaibane. Ya kuma jadda aniyar rundunan na cigaba da kare rayuka da ma dukiyoyin jama a kuma zasu cigaba da aiyuka kafada da kafada da takwarorinsu domin tabbatar da tsaro a tsakanin al umma baki daya. Kwamishina ya kirayi manyan Jami an hukumomin tsaron biyu da suyi dukkanin maiyuwa domin magance matsalar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.