IMWON shiyar jahar Gombe ta rantsar da sabbin shuwagabaninta..
Kungiyar tallafawa mata musulmai da marayu a Najeriya wato IMWON a takaice ta talafawa marayu dama baiwa mutane da dama lambar yabo a jahar Gombe.
Kungiyar ta bada lambar yabonne a Babban taronta da ta gudanar a jahar Gombe indama ta kaddanar da kungiyar, tare da rantsar da amirorin kungiyar a kananan hukumomi goma sha Daya dake fadin jahar Gombe.
Hajiya Mariya Nasiru N Ladan itace Darektar kungiyar wato IMWON ta kasa yace an shirya wannan taron me domin kaddanar da kungiyar a jahar ta Gombe tare da kaddamar da amirorin na kananan hukumomin dake fadin jahar ta Gombe
Hajiya Mariya Nasiru ta Kuma baiyana cewa a taron sun tamakawa marayu Sama da goma da takartun karatu abun rubutu jakkuna da kudade da dai sauransu.
Da wannan nema take kira ga takwaririnsu da Suma su maida hankali wajen taimakawa marayu a Koda yaushe domin Suma su samu saukin rayuwa yadda ya kamata.
Ta Kuma kirayi marayun da suyi amfani da abunda aka basu ta hanyar da ta dace domin samun nasaran karatunsu yadda ya kamata.
Itama anata jawabi Amiran Kungiyar wato IMWON a jahar Gombe Hajiya Hauwa Isa Waziri bayan taimakawa marayun an baiwa wasu mutane Sama da ashirin lambar yabo saboda irin rawa da suka taka na taimakawa Al ummar.
Hajiya Hauwa ta shawarci wadanda suka samu lambar yabon ta sucigaba da taimakawa domin ganin an samawa marassa galihu dama marayu ingancaccen raguwa a tsakanin Al umma.
Ta Kuma kirayi Amirorin kananan hukumomi da aka rantsar da sukasance masu fadada aiyukan kungiyar a kananan hukumomi da suke jagoranta domin samun cigaban kungiyar dama ganin kungiyar ta cimma manufofinta na taimakawa jama a.
Hajiya Asma au Abubakar itace Amiran Kungiyar ta IMWON a jahar Adamawa da baiyana gamsuwarta dangane da wannan taro tare da baiyana fatanta dacewa Allah madaukakin sarki ya basu kwarin gwiwan cigaban da aiyukan taimakawa Al umma.
Ta Kuma kirayi daukacin mebobin kungiyar ta IMWON dake fadin Najeriya da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe Wanda hakan zai taimaka musu wajen samun nasaran aiyukan da suka sa a gaba.
Taron dai ya samu halartan membobin kungiyar da dama wadanda suka fito daga sassa daban daban a fadin Najeriya tare da Al umma na ciki da wajen jahar ta Gombe.
Harwayau taron ya samu halartan sarakunan gargajiya daga ciki da wajen jahar ta Gombe.
Comments
Post a Comment