FOMWAN ta rabawa marayu 15o kayakin abinci Dana sawa a jahar Adamawa.
Kungiyar mata musulmai ta tarayya a Najeriya FOMWAN shiyar jahar Adamawa ta rarrabawa marayu kayakin abinci Dana sawa harma da kudade domin su samu saukin rayuwa a tsakanin Al umma.
Da take jawabi a lokacin rarraba kayakin Amiral ta FOMWAN a jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba tace duk shekara suna rabawa marayu irin wadannan kayakin a harabar makarantar FOMWAN dake nan Yola.
Hajiya Khadija Buba ta shawarci Al umma musulmai da sukasance masu taimakawa marayu a Koda yaushe domin Suma su samu saukin rayuwa musammanma a wannan wata na Ramadan.
Hajiya Khadija tace taimakawa marayu Yana da mutukan muhimmanci domin akwai lada Mai yawa daga Allah madaukakin sarki saboda haka Yana da muhimmanci a maida hankali wajen tallafawa marayu.
Itama anata jawabi darectan harkokin addinin musulunci a kungiyar ta FOMWAN shiyar jahar Adamawa Hajiya Hauwa Garba ta kirayi Al umma musulamai da su maida hankali wajen tura yara marayun makarantu zamani Dana addinin domin su samu illimin addinin Dana zamani.
Hajiya Hauwa Garba ta ja hankalin Al umma da sukasance suna kula da tarbiyar marayun yadda ya kamata a Koda yaushe domin ganin sun rayu cikin Al umma lafiya ba tare da wata matsalaba.
Ta Kuma kirayi marayun muasamman ma wadanda suka samu taimakon da sukasance suyi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace domin samun cigaba yadda ya kamata.
Wasu daga cikin wadanda suka samu taimakon sun baiyana farin cikinsu da jindadinsu dangane da irin wannan taimako da akyi musu sun Kuma tabbatar da cewa zasuyi amfani da abinda aka basu yadda yakamata.
Cikin kayaki da aka taimaka da su din dai sun hada ta kwalin taliya 15 da buhunan ahinkafa 25 da turamain zani 100 da yadi da dama da Kuma kudade ga marayun da yawansu ya Kai Sama da Dari da hamsin. 150.
Comments
Post a Comment