Gwamnatin jahar Taraba ta nemi hadaka da ma aikatar yawon shakatawa ta tarayya

 


Daga Sani Yarima Jalingo.


Gwamnatin jahar Taraba ta nemi hada Kai da ma aikatar yawon Bude ido a  Najeriya domin bunkasa harkokin yawon Bude ido da shakatawa a Najeriya.




Kwamishiniyar Muhalli da sauyin yanayi a jahar Taraba Hajiya Aisha A Barde ce ta baiyana haka a lokacinda ta ziyarci ministan ma aikatar yawon Bude ido da shakatawa a Najeriya Lola Ade John a ofishinta dake Abuja.




Kwamishiniyar da Kai ziyaranne da tawaganta dama shugaban SUNVILA NIGERIA Ibrahim Pam. Inda tace ta kawo ziyarar ne saboda Kara donkon zumunci a tsakanin ma aikatar yawon Bude ido da gwamnatin jahar Taraba domin samun damar gudanar da aiyukan bunkasa yawon shakatawa domin bunkasa tattalin Arzikin jahar, kasancewar jahar tana da wurin yawon Bude ido kamar Gashaka Gunti National Park.




Hon. Aisha Barde ta baiyana cewa aiyukan zai taimaka a bangarori daban daban da suka hada da Samar da aikinyi, cigaban Al umma, harma da inganta rayuwa Al umma da dai sauransu.



Ta Kuma ambato gwamna Agbu Kefas Yana iya kokarinsa domin inganta tsaro dama kula da tafiye tafiye a fadin jahar.




Itama anata jawabi ministar ma aikatar yawon Bude ido Lola Ade John tayi farincikin marabtar tawagan tace akwai bukatar samun hadin Kai da kyakkawar halaka da jaha domin Samar da dabaru da cigaba a Najeriya.



Ta nuna shaawarta na Samar da aiyukan cigaba da inganta harkokin yawon shakatawa a fadin Najeriya.



Ministar Lola Ade tace yana da muhimmanci a Samar da aiyukanyi Wanda hakan zai taimaka wajen Samar da kudaden shiga.




Shima anashi bangaren shugaban SUNVILA NIGERIA  ya Kuma zanyano cewa akwai aiyuka da dama da zasu taimakawa jaha da kasa baki Daya ya Kuma tabbatarwa ministan cewa wannan kamfani ya amince da bukatarta.




Kamfanin na SUNVILA NIGERIA kamfanin ne na hadin gwiwar a tsakanin kasar Koriya da Najeriya domin Samar da inganta aiyukan yawon shakatawa a tsakanin kasashen biyu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.