Wasu da ake zargin Yan fashi da makamine sun shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa.

 



A kokarinta na dakatar da aiyukan Yan fashi da masu garkuwa da mutane rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cafke mutane biyar da ake zargi da fashi da makami.


Mai magana da yawun rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


Sanarwan tace an samu nasaran kama wadanda ake zargin ne tare da hadin gwiwar mafarauta Kuma lamarin ya farune a kan hanyar da ta hada jahar Adamawa da Taraba.


An tsare wadanda ake zargin ne biyo bayan samun Kiran gaggawa dacewa an tare hanyar da ta tashi daga Numan zuwa Jalingo. Nan take aka garzaya wurinda lamarin ya faru Wanda haka yasa aka kama mutane biyar cikin bakwai.


Rundunan bayan ta gano makamai a wurin wadanda ake zargin ta Kuma ceto wadanda akayi garkuwa da su.


Kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Dankombo Morris ya bayana farin cikinsa ya Kuma yabawa SP Begina Umar wato DPO Demsa da mutanensa da mafarauta bisa namijin kokari da sukayi na kama wadanda ake zargi.


Kwamishinan ya bada umurnin gudanar da bincike kuma da zaran an kammala binciken za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE