Kungiyoyin SSANU da NASU sun bukaci gwamnatin tarayya ta biyasu Albashinsu na watanni hudu da suke bi.
Kungiyoyi manyan ma aikatan Jami o I a Najeriya SSANU da wadanda ba malumaina wato NASU na shiyar Jami ar Modibbo Adama dake yola.sun kirayi gwamnatin tarayya da tayi dukkanin abinda suka dace domin biyansu abash
insu ma watanni hudu da suke binta ko Kuma su shiga yajin aiki na gama gari na kasa baki Daya.
Shuwagabannin kungiyoyin biyu ne suka baiyana haka a lokacinda suke gudanar da zanga zangan lumana a harabar Jami ar Modibbo Adama dake Yola.
Shugaban kungiyar manyan ma aikatan Jami o I wato SSANU shiyar Jami ar Modibbo Adama a Yola Comrade Michael I Omokoro yace sun gudanar da zanga zangan Lumanan ne domin su nuna rashin Jin dadinsa da biris da su da gwamnatin tarayya tayi na kin biyansu Albaahinsu na watanni hudu da suke bin gwamnatin ta tarayya.
Don haka suna masu Kiran gwamnatin da ta cika alkawura da Kuma mutunta yarjejeniya da sukayi na cewa zata biyasu Albaahinsu, to ya kamata ta aiwatar da yarjejeniyar domin kaucewa shiga yajin aiki na kasa baki Daya.
Comrade Omokoro yace sun shiga yajin aiki na gargadi amman gwamnatin bata biyasuba saboda yake kira ga shugaban kasa da yayi dukkanin Mai yiwa domin ganin an biyasu Albaahinsu na watanni hudu da suke bin gwamnatin tarayya.
Itama anata bangaren shugaban kungiyar ma aikata da ba malamaina NASU shiyara Jami ar Modibbo Adama dake Yola Comrade Sadiya Mustafa itama ta kirayi gwamnatin tarayyar da tayi la akari da bukatunsu Wanda acewarta yin haka zaitaimaka wajen samun cigaban aiyukan Jami o I dake fadin kasa nan.
Comrade Sadiya tace an dauki tsawon lokaci ana tattaunawa da gwamnatin tarayya dama masu ruwa da tsaki dangane da matsalar amman har kawo yanzu haka bata cimma ruwaba, saboda haka ya kamata gwamnati ta duba ta dauki matakin magance matsalar.
Comrade Sadiya tace in harfa gwamnatin ta biyasu albashinsu da suke bi na watanni hudu to suna iya dakatar da yajin aiki da suka kudiri aniyar yi in Kuma ba a biyasuba to basu da zabi illa su shiga yajin aiki na saibaba ya gani.
Saboda haka zabi ya ragewa gwamnati wajen daukan matakai da suka kamata domin biyan membobin kungiyoyin biyu da suka lashi takwabin shiga yajin aiki in har basu samu biyan bukataba.
Comments
Post a Comment