A nemi da gwamnatin tarayya ta Samar da hukumar da zata sanya ido kan harkokin aiyukan kwale kwale a fadin Najeriya.

 






An bukaci gwamnatin tarayya da ta Samar da hukumar da zata sanya ido kan harkokin masu amfani da kwale kwale a fadin Najeriya domin magance yawan hadura kwale kwale da ake samu a wasu sassan Najeriya.


Sarkin ruwan Geriyo a jahar Adamawa Alhaji AbdulRazak Abubakar me yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


.Alhajiya AbdulRazak Abubakar yace Samar da hukumar zai taimaka matuka duba da irin yawan hadura da ake samu Wanda yake sanadiyar rasa rayuka da dama saboda haka ya kamata gwamnatin ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin domin dakile matsalar.



Abubakar ya kuma ja hankalin masu yin amfani da kwale kwalen da su kaucewa akata ganganci domin acewarsa akasari lamarin na aukuwane sakamokon aikata Yanganci.


Saboda haka nema ya shawarcesu da su daina diban kaya ko fasinjoji fiye da kima saboda diban kaya daidai wadaida zaitaimaka wajen rage yawan hatsarin kwale kwale.


Sarkin ruwan ya Kuma jajantawa iyalen wadanda suka rasa rayukansu sakamokon hatsarin kwale kwale da ya faru a jahar Neja dama sauran sassan Najeriya Allah ya baiwa wadanda suka jikkata lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.