Gwamnatin jahar Adamawa ta kirayi manoma da makiyaya da su rungumi zaman lafiya da hadin Kai a tsakaninsu.











 An kirayi manoma a jahar Adamawa da sukasance masu bin dokokim da aka gindaya domin ganin an samun cigaban bunkasa harkokin noma da kiyo domin samun cigaba harma da wanzar da zaman lafiya Mai daurewa a fadin jahar.





Babban sakataren harkokin tsaro a gidan gwamnati dake Nan Yola  Alhaji Usman Suleiman Palam ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola.





Alhaji Usman Suleiman Palam yace ya kamata manoma su kaucewa shuka ko noma a burtalai shanu ko wurin kiwo domin kaucewa rikici a tsakanin manoma da makiyaya.



Suleiman Palam yace manoma da makiyaya su sanifa su Yan uwan juna ne, sanda haka Bai kamata ace an samu tashin hankali a tsakaninsuba, saboda tashin hankali a tsakanin manoma da makiyaya koma baya ne sosai a nangarorin noma dama kiwo.



Palam ya Kuma shawarci manoma da  da sukasance suna shuka tsakaninsu da hanya ya Kai mita talatin    domin baiwa hanya hakkinsa da wannan ne yake shawartan manoma da makiyaya da sukasance masu hada kansu da Kuma taimakawa juna domin ganin an samu zaman lafiya ma daurewa.




Ya Kuma jaddada aniyar gwamnatin nayin dukkanin abinda suka dace domin ganin an samu zaman lafiya Mai daurewa a tsakanin manoma da makiyaya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT