DR SQLIHU BUKARI GIREI YA GUDANAR DA AIYUKAN CIGABA HARMA DA SAMARWA MATASA AIKINYI A LOOACIN DA YAKE RIKE DA MUKAMIN KWAMISHINA.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.



Dr Salihu Bukari Girei a zamanin da yake kwamishinan kananan hukumomi da sarakuna a jahar Adamawa ya taka rawan gaban hantsi wajen gudanar da aiyukan cigaban Al umma a bangarori daban daban a fadin jahar Adamawa.


Bangarori da Dr Salihu Bukari Girei ya kawo cigabansu a jahar Adamawa sun hada da bangaren. Ilimi, kiwon lafiya, sanarwa matasa aikinyi, bunkasa harkokin noma, Samar da tsfcacaccen ruwan Sha, musammanma a yankunan karkara, wutan lantarki, koyar da kananan sana o I wa matasa da mata da dai sauransu.


A bangaren ilimi Dr Salihu Bukari Girei yasa an fadada Gina makarantun a dinkanin kananan hukumomi a Shirin da Daya dake fadin jahar Adamawa, Wanda hakan yasa Yara da dama daga sassa daban daban dake fadin jahar sun samu inganceccen ilimi a fannoni daban daban.


Dr Salihu Bukari Girei Bai tsaya ananba ya Samar da ciniyoyin kiwon lafiya domin kula da kiwon lafiyar Al umma a matakin farko domin ganin kowa ya samu wadaceccen kiwon lafiya yadda ya kamata a dukkanin kananan hukumomi.




Dr Salihu baiyi kasa a gwiwaba wajen koyawa matasa da mata kananan sana o I daban da suka hada da tela, kiwo, makanikanci, noma, da dai sauransu. harma da samarwa matasan aiyukanyi a ma aikatu daban daban a fadin jahar ta Adamawa.



Dr Salihu Bukari ya bunkasa harkokin noma ta taimakawa manoma da kayakin noma irinsu taki, maganin feshi, inganceccen iri, Wanda hakan ya baiwa manoma dake fadin jahar daman bunkasa harkokin noma dama Samar da inganceccen abinci a fadin jahar.


A bangaren  bunkasa tattalin Arziki kuwa Dr Salihu Bukari Girei ya taka rawan ganin wajen kirkiro dabaru daban daban domin Samar da kudaden shiga a dukkanin kananan hukumomi dake fadin jahar.


Saboda haka nema Dr Salihu Bukari Girei ya kudiri aniyar tsayawa takaran gwamna a zaben shekara ta 2027 domin ganin ya cimma burinsa na bunkasa tattalin arzikin jahar Adamawa, da Samarwa matasa aikinyi harma da inganta zaman lafiya da dai sauransu a fadin jahar.



Dr Salihu Bukari yace a shirye yake idan an bashi daman zama gwamnan jahar Adamawa zaiyi dukkanin abinda suka dace domin cigaban Al ummar jahar dama jahar baki Daya. Wadanada suka hada inganta kayakin more rayuwa, gine gine da gyra hanyoyi musamman a yankunan karkara da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT