One ummah ta rarranawa marayu kayakin abinci Ramadan a Jahar Adamawa tare da Kiran masu hanu da shuni su taimakawa marayu.

 





Daga Alhassan Haladu Yola.


Domin inganta rayuwar marayu, an kirayi masu hanu da shuni da sukasance sun taimakawa marayu domin Suma su Samu saukin rayuwa a tsakanin Al umma baki Daya.


Hajiya Amina Kabir Wanda ma itace shugaban kwamitin taimakawa marayu ma one ummah karkashin jagorancin Women in Da awa dake jahar Adamawa ne tayi wannan Kira a lokacin da suke taimakawa marayu kayakin abinci da zasu gudanar da Azumin watan Ramadan.



Hajiya Amina Kabir tace sun dauki matakin taimakawa marayu ne biyo bayan fadin manzon Allah tsra da amincin Allah su tabbatar agaresh yace taimakawa marayu abune da yake da matukan muhimmanci da Kuma Samun Lada mai yawa.


Ta Kuma shawarci marayun da suyi anfani da abinda aka basu domin Samun cigaban dama inganta rayuwarsu yadda ya Kamata, ba tare da wata matsalaba.



Hajiya Amina tayi Adu ar Allah madaukakin sarki  da ya jikan iyayensu su Kuma Allah ya ba su hakurin  jimre Rashi da sukayi.



Itama anata bangaren Daya daga cikin iyayen marayun mata Malama Zainab Yahaya ta baiyana godiyarta da Jin dadinta dangane da wannan taimakao da suka Samu, inda tayi Adu ar Allah ya sakawa one ummah da Alheri.


A cewarsa dai yazan dole su godewa one ummah domin sun dauki tsawon ahekaru suna taimakawa marayu a bangarori daban daban da suka hada da ilimi, koyar da sana o I, taimakawa da kayan sawa, kayakin abinci da dai sauramsu.


Wasu daga cikin marayun da suka Samu taimakon sun baiyana godiyarsu da Jin dadinsu dangane da wannan taimako da aka basu tare da tabbatar da cewa zasu anfani dashi yadda ya Kamata.


Suke one ummah ta taimaka musu a bangarori daban ciki harda kaisu birnin tarayya Abuja  inda suka gudanar da Gaza Wanda hakan ya taimaka musu kwarai  lamarinda ke Sanya musu farin ciki a Koda yaushe.


Sun Kuma kirayi sauran kungiyoyi da ma masu hanu da shuni da suyi koyi da one ummah wajen taimakawa marayu domin ganin marayun sun Samu saukin rayuwa a tsakanin Al ummah.



Ckin kayakin da aka rarraban dai sun hada da shinkafa, wake, main gyada, maggi, gishiri, suga da dai sauransu.


Sama da marayu tamanin da hudu ne dai suka karbi kayakin abinci daga One ummah.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie