Gidauniyar HUG ya taimakawa mata 30 domin sana ar dogaro dakai a karamar hukumar Yola ta kudu.

Gidauniyar Hamidu Umaru Gulak Wanda akafi sani da HUG. Ya taimakawa mata akalla talatin a cikin karamar hukumar Yola ta kudu dake jahar Adamawa da kudaden sana o I domin su dogara da kansu da iyalensu dama Al umma baki Daya. Gidauniyar ya fahinci cewa akwai bukatan karfafawa matan domin su bunkasa harkokin kasuwancinsu domin rage musu radadin wahalar rayuwa da suke cikin duba da yadda ake samun matsalar rayuwa a fadin kasan nan. An zakulo wadanda suka cigajiyar Shirin daga cikin Al ummomin dake cikin karamar hukumar Yola ta kudu wadanda suka samu taimakon kudade da suka kama daga dubu 20,000 da 30,000 da kuma dubu 50,000 wanda acewarsu hakan zai taimaka musu na tsawon lokacin da Kuma bunkasa musu kasuwancinsu. Da yake yiwa wadanda suka ci gajiyar Shirin Mudas Mai Karfe Wanda malami ne a jami ar modibbo Adama yace nan gaba ma za a taimakawa manoma. Inda ya kirayi wadanda suka amfani da taimakon da suyi amfani da shi yadda ya kamata domin samun cigaba. Daya daga cikin wadanda...