An baiyana irin muhimmanci da karatun Al qur ani mai girma yake dashi a tsakanin al ummah musulmai.

An kirayi Al ummah musulmai da su kara himma wajen gudanar da karatun All qur ani kai girma domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya kamata a tsakanin Al ummah musulmai baki daya. Alhaji Sadiq Umar Daware ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin rufe gasar karatun Al qur ani mai girma wanda kungiyar gaskiya TV Africa shiyar jahar Adamawa ta shirya a yola. Alhaji Sadiq Daware wanda shine shugaban bikin yace karatun Al qur ani dama karantarwa yana da mutukan muhimmanci a tsakanin Al umma musulmai don haka akwai bukatan al umma musulmai sukasance masu runguman karatun Al qur ani domin samun daman yada addinin musulunci. Alhaji Daware ya kuma yabawa kungiyar ta Gaskiya TV bisa shirya wannan gasar karatun al qur ani mai girma ya kuma yi fatan zasu fadada aiyukansu har zuwa nahiyar Afirka baki daya. Ya kara kira ga al umma musulmai musammanma kungiyoyin addinin musulunci da suyi kasance masu shirya gasar karatun al qur ani mai girma domin samun cigaban addinin musulunci bak daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE