An bukaci iyaye su kara kaimi wajen tura yaransu islamiyoyi.

An ja hankalin iyaye da su maida jankali wajen tura yaransu makarantu domon koyon karatun Al qur ani maigirma domin ganin an samu cigaban karatun al qur ani a tsakanin yara baki daya. Alhaji Sadiq Umar Daware ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin bikin kammala gasar karatun Al qur ani maigirma wanda Gaskiya TV afirka ta shirya a yola. Alhaji Sadiq Daware shinema shugaban taron yace koyar da yara karatun Al qur ani tun suna yara yana da matukan muhimmanci don haka yakamata iyaye su tashi tsaye wajen baiwa yaransu ilimin karatun Al qur ani domin samun cigaban addinin musulunci. Ya kuma yabawa kungiyar ta gaskiya TV da ta shirya wannan gasa kuma ya kirayi sauran kungiyoyin addinin musulunci da su cigaba da shirya irin wannan gasa wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimin addini da ma karatun Al qur ani maigirma. Ya Kara jaddada goyon bayansa a duk lokacin da aka bukaci taimakonsa tare da shawartan al umma musulmai da sukasance masu hada Kansu da kuma cigaba dayin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki waken kawo dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya. Shima a jawabinsa shugaban kungiyar ta gaskiya TV a jahar Adamawa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ya baiyana farin cikinsa dagane da yadda aka kammala gasar lafiya ba tare da matsalaba. Don haka ya godewa malamai da ko oditotin da suka gudanar da wannan gasa. Ya kuma kirayi iyaye da su basu hadin kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na faada karatun Al qur ani a tsakanin yaran yadda ya kamata. Da yake nashi jawabi Mallam Sahabo Magaji ya nuna jin dadinsa dangane da yadda dalube suka halarcin gasar karatun Al qur ani don haka akwaibukata hadinkan al umma musulmai wajen wajen baiwa yara karatun al qur ani maigirma. An kuma kadamar da shuwagabanin da zasu ja ragamar kunguyar ta gaskiya TV a jahar Adamawa, wadanda suka hada da Alhaji Muhammed Ibrahim 86 a matsayin shugaba sai Alhbaji Musa iliya mataimakin shugaba na daya a yayinda Alhaji Hassan Muhammed Sallau mataimakin sugaba na biyu shikuwa Adam A Adam sakatare da Alhaji Suleiman Adamu shine mataimakin sakatare, sauran sun hada da Hamza Abdullahi a matsayin sakataren kudi, Ustas Abdullahi Hassan Imam ma aji da Nazir Buba sakataren tsare tsare da Ibrahim Abdullahi mai bincike na daya, sai Mustafa Umar mai bincike na biyu , Hassan Umar Shallpella shine P R O da kuma Alhaji Ibrahim Miyetti P R O na biyu. Sai kuma Muhammed Isa Muhammed a matsayin memba. A bangarena mata kuwa an kaddamar Hajiya Aisha Khamis a matsayin Amira, Hajiya Safiya Mohammed mataimakiyar Amira, da malama Fatima Mamman sakatarya, da Mufassira Asiya Jibril sakatariyar tsare tsare, Hon. Amina Abubakar Gangfada ma aji. Da yake magana jin kadan da kaddamar da shuwagabannin wanda shinema ya kaddamar da sabbin shuwagabanin, Wakilin Gurin wandama shine hakimin Gurin Alhaji Abubakar Abbo Baba Gurin ya kirayi shuwagabannin da su gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin samun cigaban kungiyar dama bunkasa karatun Al qur ani a tsakanin Al umma musulmai. Da yake magana a madadin sabbin shuwagabannin Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ya tabbatar da cewa zasu gudanar da aiyukansu bilakki da gaskiya domin ganin sun cimma burinsu na ilimantar da yara karatun Al qur ani mai girma. Dalube da dama ne dai wadanda suka fito daga kananan hukumomi ashirin daya dake fadin jahar Adamawa suka shiga gasar wanda kuma Gazzali Bala daga karamar hukumar Mayo Belawa ne ya kasance gwarzon shekara a gasar sai kuma Fatima Yunus Adam daga karamar hukumar Tongo ta zama gwarzuwa shekara. Sun kuma baiyana farin cikinsu dangane da shirya wannan gasar karatun Al qur ani maigirma, wanda acewarsu hakan zai taimaka wajen karawa daluben kwarin gwiwar karatun Al qur ani.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.