An horar da dalube harkokin wasanni daban daban a jahar Taraba.
Daga Sani Yarima Jalingo.
An shawarci musammanma dalube da sukasance masu neman ilimin wasan badminton domin su zama masu gudanar da irin wasanin a fadon duniya.
Darectan wasannin jahar Taraba George Shitta ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake jawabi a wurin bikin kamala horar da daluben sakandare wasan badminton da aka dauki tsawon kwanaki uku anayi a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba.
Dalube tamanin daga makarantun sakandare tamanin ne dai da suka da gwamnati harma da masu zaman kansu suka samu haron wasanni daban daban akalla ashirin da hudu.
Shitta ya shaidawa manema labarai cewa wata kungiya mai zaman kanta wato kungiyar bunkasa wassani da ilimantarwa a cikin al umma CSED tare da hadin gwiwar sashin wasan badminton a jahar Taraba ne suka dauki nauyin.
Yace sun dauki matakin horan da daluben ne domin zaburan da matasa dama bunkasa harkokin wassani a jahar ta Taraba.
Darektan ya kuma yaba da yadda kungiyar da zabi jahar Taraba domin horan da daluben wanda acewarsa wannan cigabane sosai ga gwamnati dama al ummar jahar baki daya.
George ya kuma baiyqna cewa kungiyar ta taimaka da kayakin wasanni daban daban wanda hakan zai karawa daluben kwarin gwiwar bunkasa harkokin wasanni a fadin jahar Taraba baki daya.
A zantawarsa da manema labarai darekto a ma aikatan wasanni dake jahar Taraba Mr Affos Musa Emmanuel yayi alkawarin ganin an samu Karin masu horar da dalube da zasu ronka zuwa malarantu domin horar da daluben wasanni.
Wasu daga cikin wadanda suka samu horon sun baiyana farin cikinsu dangane da wannan horo da akayi musu tare da tabbatar da cewa zasu amfanin da abinda aka koya musu yadda ya kamata domin cigaban wasanni a fadin jahar baki daya.
Comments
Post a Comment