An kirayi mazauna gundumar Nasarawo Abba da sukasance masu hada kansu.
An kirayi mazauna gundumar Nasarawo Abba dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin samun cigaban gundumar harma da samar da zaman lafiya a gundumar baki daya.
Hakimin Nasarawa Abba kuma sarkin sudan Adamawa Alhaji Abubakar Aliyu Mustafa ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a dai dai lokacinda wadanda suka samu sarautun gargajiya a gundumar na Nasarawo Abba suka kaimasa ziyaran godiya a fadarsa dake Nasarawo Abba.
Hakimin yace hadin kai a tsakanin al umma abune da yake da mutukam muhimkanci don haka akwai buktan al umma su kasance masu yin dukkanin abunda suka dace domin hadin kai dama cigaba.
Alhaji Abubakar Aliyu Mustafa ya shawarci al umma gundumar ta Nasarawo Abba da su bashi hadin kai da goyon baya domin ganin an wanzar da zaman lafiya dama cigaban gundumar baki daya.
Ya kirayi wadanda suka samu mikamen masarautun gargajiya da su gydanar da aiyukansu bilhakki da gaskiya da kuma aiki kafada da kafada domin ganin an samu wadaceccen tsaro a gundumar ta Nasarawo Abba harma da jahar dama kasa baki daya.
A jawabinsa na godiya a madadin wadanda suka samu mukamen gargajiya mai jimillan Nasarawo Muhammed Suwidi Bello ya nuna gidiyarsa dangane da samar da mukamen masarautun gargajiya yace a shirye suke suyi aiki tare da kuma bada hadin kai domin samun cigaban gundumar ta Nasarawo Abba.
Cikin wadanda suka samu mkamen sarautar gargajiyar dai sun hada da Babangida Babainna a matsayin sarkin matasan gundumar Nasarawo Abba da Ummar Ibarahim wanda akafi sani da Bappa. Da dai sauransu.
Comments
Post a Comment