An kirayi yan jarida da su sanya tsoron Allah a zukatansu a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu.
Daga Sani Yarima Jalingo.
An jawo hankalin Yan Jarida da suji tsoron Allah wajen kaucewa bada labarin da zai kawo tashin hankali a kasa, musamman a wannan lokacin da zabuka ke karatowa a wannan shekaran.
Tsonhon Mukaddashin Gwamnan Jihar Taraba, Sanata Sani Abubakar Danladi yayi wannan kiran alokacin da yake amsa tambayoyin daga manema labarai a garin Jalingo.fadar gwamaatin jahar Taraba.
Tsonhon Mukaddashin Gwamnan kuma tsonhon Sanata, Malam Sani Abubakar Danladi yace idan har Yan Jarida zasu tsaya kan gaskiya wajen bada labarai yadda suke, toh babu shakka za'a samu. zaman lafiya a Jihar dama kasar Najeriya baki daya.
"Yanzu zan jawo hankalin Kun tunda kuka yimini wannan tambayan kace abinda baku iya tambaya in bada amsa toh kuma zan bada amsa, don Allah ku tsaya tsakanin ku da Allah ku bada rahoton abinda kuka san bazai tada hankalin kasa ba.
"Domin yawaci matsaloli kashi chasa'in da Tara (99%) daga wurin ku yake fitowa, abinda wani bai fada ba sai kuje ku ruruta wuta, to kuji tsoron Allah ranan gobe Allah zai tambayeka, in kafadi alheri toh zakaga alheri kuma Inka fadi sharri zaka ga sharri.
"Sannan kuma mu Yan siyasa duk wani abunda kuke ganin mu a yanzu kowa ya waye, ba wanda zaiso ace ba zamu so mu zauna lafiya da juna ba. Ina mana addu'a dukkan mu da Yan siyasan da ku yan jaridun dama da talakawa daza su jefa kuri'a ubangiji Allah ya bamu hikima da basira da zaman lafiya a Taraba dama Najeriya baki daya, da fatan za'ayi zabe lafiya ba tareda anjima kowaba sabanin yadda wasu ke harshashen rikici.
Malam Sani Abubakar Danladi ya sami nasaran samun tikitin tsayawa takaran Sanata a zaben 2023 mai zuwa wanda kotun dauka kara dake zamanta a Yola, fadan jihar Adamawa ta tabbatar mishi bisa abokin takaran sa, Alhaji Ali Sani Kona.
Danganeda da yadda yaji na samun nasaran da yayi a kotun dauka ka kara dake zaman ta a Yola, fadan jihar Adamawa Sanata Danaldi yace "bani da abinda zance saide inyi godiya ga Allah na farko, da kuma in godewa kotu na daukaka kara da ta tsaya tayi gaskiya kuma inada yakinin sunyi gaskiya kuma na yarda sun fitar da gaskiya, shiyasa nake jinjina musu."
Sanata Sani Abubakar Danladi sami nasaran samun tikitin tsayawa takaran ne a karkashin Jam'iyyar APC inda suka fafata da Alhaji Ali Sani Kona alokacin zaben fidda gwani.
Kazalika ya roki abokan takaran sa dasu dauki hukuncin daga Allah ne suzo su hada kai domin samar wa Al'umma abubuwan cigaba, tare da rokon duk Wanda ya Saba masa daya yafe masa, yana mai cewa a yanzu babu abinda yake nema illa ya tsaida gaskiya domin ya rike mukamai daban daban.
Sanata Sani Abubakar Danladi ya kuma godewa al'umman Jalingo, Yerro, Zing, da Karim Lamido bisa irin goyon baya da karrama shi da suke yi, yana mai cewa da yardan Allah bazaici amanan su ba domin yayi sun gani.
Malam Sani Abubakar Danladi ya rike mukaman siyasa da dama, tunka kansila, shugaban karamar hukumar Karim Lamido zuwa Mataimakin gwamna sau biyu a zamanin tsonhon Gwamnan Jihar, marigayi Danbaba Suntai kafin ya zama Mukaddashin Gwamna inda daka bisani aka zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltan Taraba ta Arewa a Majalisar Daddatawa mu kamin da ayanzu haka yake nema ya koma bisa amsa kiran talakawa.
Comments
Post a Comment