An nada mace ta farko a matsayin waziriyar Song.
An nada hajiya Aishatu Abubakar Ahmed Song a matsayin waziriyar Song wanda kuma itace mace ta farko da fadar hakimin song din ya ta a matsayin waziriya.
An dai gudanar da bikin nadinne a fadar hakimin song wato Ahmed Sa idu wanda ya samu halartar yan uwa da abokan Arziki na ciki da wajen karamar hukumar Song dake jahar Adamawa.
Da yake nadata hakimin na Song Ahmed Sa idu ya kirayi waziriyar da ta kasance mai baiwa masarautar hadin kai da goyon baya domin ganin samun cigaban masarautar dama hadin kan masarautar harma da al umar karamar hukumar dama jaha baki daya.
Hakimin yace an nadatane biyo bayan irin gudumawa da take baiwa masarautar don haka ya shwarceta da ta kare martabarta dana masarautar domin samun cigaban masarautar harma da wanzar da zaman lafiya.
Harwayau ya kirayeta da ta kasance mai nuna halaye ta gari a dukkanin lamuranta a koda yaushe dama cigaba da bada hadin kai da goyon baya ga masarautar wanda a cewarsa haka zai taimaka wajen hadinkan masarautar baki daya.
Da take magana a madadin sabuwar waziriyar ta Song hajiya Aishatu Umar Bamanga ta godewa hakimin bisa baiwa Hajiya Aishatu Abubakar Ahmed Song.wanda ta zama daya daga cikin wadanda ke rike da masarautun gargajiya a fadar ta hakimin Song.
Hajiya Aishatu Abubakar Ahmed Song ta sha alwashin ganin ta yi dukkanin abunda suka dace domin ganin an samu cigaba dama hadin kai harma da wanzar da zaman lafiya a fadar dama karamar hukumar harma da jaha baki daya.
Hajiya Aishatu Abubakar Ahmed Song dai darectace a hukumar dake kula da kananan hukumomi a jahar Adamawa.
An dai gudanar da adu o i na musamman domin wanzar da zaman lafiya a jaha dama kasa baki daya. Tare da shirya liyafa wanda yan uwa da abokan arziki suka shiraya a karamar hukumar ta Song.
Comments
Post a Comment