An shawarci yan agaji da sukasance masu taimakawa al ummah.
An shawarci yan agajin fityanul Islam da sukasance masu taimakawa al umma a bangarori daban daban musammanma a bangaren kiwon lafiya domin samun cigaban yadda ya Kamata.
Darektan yan agajin fityanul Islam na jahar Adamawa Alhaji Sa idu Modibbo Buba ne ya bada wannan shawara a lokacinda yake jawabi a wurin rufe taron karawa juna sanin wanda aka shiryawa yan agajin anan yola.
Alhaji Sa idu yace an shirya wannan taronne domin karawa yan agajin sanin makaman aiki da kuma yadda zasu maida hankali wajen taimakawa al umma a bangarori daban daban.
Ya kuma kirayi yan agaji da sukasance masu nuna da a a duk lokacin da suke gudanar da aiyukansu domin samun cigaban kungiyar a tsakanin al umma baki daya.
Alhaji Sa idu ya kirayi yan Najeriya da sucigaba da yin adu oi domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki daya.
Comments
Post a Comment