An yaba da shugabanci shugaban karamar hukumar Girei dake jahar Adamawa.

An yabawa shugabancin karamar hukumar Girei dake jahar Adamawa Hon. Juda Amisa garkuwar Luru tafida. Tambo. bisa yadda yake gudanar da aiyukan cigaban karamar hukumar dama cigaban karamar hukumar. Muhammed Muratalan ya yi wannan yabo a lokacinda ya zantawa da jaridar All Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Muhammed Murtala yace Him. Juda ya gudanar da aiyukan cigaban Al ummar karamar hukumar ta Girei a bangarori daban daban da suka hada da gina asibitoci, makarantu, Bohol Bohol, hanyoyi, bunkasa harkokin noma, da kiwo zaman lafiya da dai sauransu. Murtala ya kuma baiyana cewa Juda mutumne da ya san makaman shugabanci saboda yayi kansila har sau biyu ya rike mukamin shuhaban majalisar kasinlolin karamar hukumar ta Girei, ya kuma yi mataimakin shugaban karamar hukumar Girei haka kazalika ya yi shugabancin karamar hukumar Girei sau biyu, saboda haka ya kware wajen gudanar da shugabanci da kuma gudanar da aiyukan cigaban Al ummah. Don haka nema yake shaidawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa cewa ya samu jajirceccen shugaban karamar hukumar a Girei Wanda ya sadaukar da kansa wajen yiwa Al ummarsa aiki ba dare ba rana. A bangaren samar da aiki kuwa Hon. Juda ya samarwa matasa aiki a wani mataki na rage rashin aikinyi a tsakanin matasan karamar hukumar ta Girei a jahar ta Adamawa. Saboda haka Muhammed Murtala yake kira ga daukacin Al ummar karamar hukumar ta Girei da sukasance masu baiwa Hon. Juda Amisa hadin kai da goyon baya domin ganin ya cimma burinsa na bunkasa aiyukan cigaban karamar hukumar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.