An yabawa gwamnnatin tarayya dangane da karantar da daluben firamare harshen uwa.

An yabawa gwamnatin tarayya bisa amincewa da a kararantar da daluben makarantin fimare da harshen uwa wanda hakan cigabane matuka. Alhaji Adamu Jingi yace gaskiya lamarin yayi dai dai wanda acewarsa ko kasashe da sukaci gaba a duniya suna karantar da dalubene da harshensu domon daluben su fahinci abinda ake koya musu yadda ya kamata. Don haka abinda gwamnatin tarayya tayi yayi dai dai kuma dafatan za a fadadashi zuwa makarantun gaba da firamare da kwalejoji harma da Jami o i domin hakane zai tai maka musammanma a bangaren likitoci, injiniyoyi, kimiya da fasaha da dai sauransu. Ya kuma kirayi masu ruwa da tsaki da sukasance masu bada hadin kai da goyon baya domin ganin gwamnatin ta cimma burinta na baiwa dalube inganceccen ilimi yadda ya kamata. Alhaji Jingi ya shawarci malamai makarantu musaman na firamare da su maida hankali sosai wajen karantar da dalube yadda ya kamata da kuma bin tsarin karantarwa wanda acewarsa hakan zai taimakawa daluben samun inganceccen karatu. Harwayau ya kirayi iyaye da su bada tasu gudumawa wajen karantar da yaran nasu ba tare da wata matsalaba domin acewarsa iyaye su suke da kaso mafi tsoka wajen baiwa yara tarbiya dama karatunsu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE