Gidaje hudu da shaguna sha daya ne aka kona a wani rikicin kabilanci a karamar hukumar lamurde dake jahar Adamawa.

A kalla gidaje hudu tare da shaguna sha daya aka kona biyo bayan sabon rikicin kabilanci da ya barke a karamar hukumar Lamurde dake jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SPSuleiman Yahaya Nguroje ya tabbatarwa Jaridar Al Nur akuwar lamarin inda yace rikicin dai ya farune a tsanin kabilar waja da lunguda kawo yanzuma ana cigaba da gudanan da bincike domin gano musabbabin tashin rikicin da kuma gano wadanda ke da hanu a cikin rikicin. So Suleiman yace da jin labarin tashin rikicin hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Sikiru Kayode Akande baiyi kasa a gwiwaba wajen tura Jami an yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru domin kwantar da rikicin. Suleiman Yahaya yace an tattauna da masu ruwa da tsaki da suka hada birget kwamanda na sojoji shuwagabanin kananan hukumomin Lamurde da Guyuk da sarakunan gargajiyan yankin harma da matasa a wani mataki na kwantar da rikicin baki daya. A yanzu haka dai kura ta lafiya biyo bayan tura Jami an tsaro a yankin wanda suke gudanar da sintiri. har zuwa hada wannan labarin ba rahoton wanda ya rasa ramsa ko jikkata a rikicin. Ya kuma kirayi mazauna yankin da suyiwa kansu kiyamul laili don kuwa runduna a shirye take ta Shiva kafar wando daya ga duk wanda ya karya doka. Kuma duk wanda aka samu da hanu a cikin rikicin to yayi kuka da kansa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE