Gidan Rediyo Najeriya fombina fm yola ya jajintawa Uba Dan Arewa.

Tawagan gidan Rediyon Najeriya Fombina FM yola sun kai ziyaran ta aziyar ga Uba Dan Arewa biyo bayan rasuwar mahaifins wato Alhaji Muhammed Dan malam Lau. Tawagan wanda Babban Manajan gidan Rediyo Najeriya fombina FM yola Alhaji Dahiru Garba Muhammed ya jagoranta. Inda yayi adu ar Alla madaukakin sarki ya jikansa ya kuma yi masa rahama yasa Aljannace makomansa. Yace a madadin gidan rediyo fombina yana mika ta aziyara ga iyalen marigayi inda ya baiyana rasuwar babban asarace baga iyalensa kawaiba harma da al ummah baki daya. Dayake jawabi a madadin iyalen marigayin wato Uba Dan Arewa ya nunu godiyarsa da jin dadinsa dangane da wannan ziyaran ta aziya wanda tawagan rediyo fombina suka kawo masa. Ya kuma yi adu ar Allah ma daukakin sarki ya bar zumunci tare dayin fatan Alheri ga ma aikata dama gidan resiyon baki daya. Alhaji Muhammed Dan Malam Lau dai ya rasune sakamokon gajeruwar rashin lafiya a cikin garin Lau dake jahar Taraba. Kuma ya rasu yana da shekaru casa in da biyu da haifuwa. Ya bar yara talatin da hudu tare da jikoki dari.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE