Gwamna fintiri ya mika ta aziyarsa dangane da mutuwar Rodney Nathan.
Gwamanan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintin ya jajintawa shuwagabanin kungiyar malamai ta kasa N U T shipyard jahar Adamawa biyo bayan rasuwa shugaban kungiyar na jahar Adamawa kwamuret Rodney Nathan.
Gwamnan ya mika ta aziyarsane a wata sanarwa daga sakataren watsa labarainsa Humwashi Wonosikou, inda inda ya baiyyana mutuwar Nathan a matsayin Babban rashine ga kungiyar ta N U T harma da Jahar Adamawa baki daya.
Gwamnan ya kuma jajantawa Iyalen marigayin dama yan uwa da abokan arziki, gwamna fintiri ya baiyana marigayi a matsayin wanda ya taka rawan ganin wajen bunkasa ilimi tare da nuna kwazo a lokacin da yake gudanar da aiyukansa.
Sanarwa ta ci gaba da cewa marigayi Rodney Nathan ya zama abun koyi ga rayuwarsa don kuwa ya bar babban gibi domin mutunne da ya da yake da muradun cigaban ilimi.
Maragayi Rodney Nathan dai ya mutu a ranan talata sakamokon rashin lafiya da yayi fama da ita kuma ya mutune a Jos dake jahar filato. Kafin rasuwarsa dai shine shugaban kungiyar malamai ta kasa N U T shiyar jahar Adamawa,kuma shugabane a yankin arewacin Najeriya da ya kunshi jihohi sha Tara. Harwa yau shine mataimakin shugaban kungiyar kwaigo wato N L C a jahar Adamawa.
Gwamnan yayi adu ar Allah ya baiwa iyalensa dama yan uwa da abokan arziki jimre hakurin rashi da akayi.
Comments
Post a Comment