Hukumar zabe ta gamsu da yadda ake karban katin zabe a jahar Adamawa.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC shiyar jahar Adamawa. ta baiyana gamsuwarta dangane da yadda al umma ke ta tururuwa zuwa karban Katin zabensu daga ofisoshin hukumar dake fadin jahar ta Adamawa baki daya. Mukaddashin kwamishinan hukumar zaben jahar Adamawa Jibril El yakub ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola. Muakaddashin kwamishinan yace biyo bayan hada kai da sukayi da kungiyoyi shuwagabannin al umma harma da masu ruwa da tsaki domin fadakar da al umma musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe da su gaggauta zuwa ofishin hukumar dake kanaan hukumomi dake fadin jahar domin karban katin zabensu. A cewarsa dai hukumar ta INEC a fara bada katin zabe daga watan disemba wanda zata dakatar da bada katin a ranan 22-1-2023. Wasu daga cikin wadanda suka karbi katinsu sun baiyyanawa manema labarai yadda suka gamsu da yadda ake bada katin zaben duk dacewa ana samun kura kure domin wasu basuga katinsuba wanda aka shaida musu su sake dawo kafinnan an warware matsalar. Hukumar Zabe tace zatayi dukkanin abunda ya dace domin ganin dukkanin wadanda sukayi rijista su samu katinsu kafin zaben shekara ta 2023.
F

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE