Kugiyar Malamain Jami o i a Najeriya ASUU tace karin kudin makarta da hwamnati tayi baizo mata da mamakiba.

Kungiyar malamai Jami o i a Najeriya wato ASUU shiyar Jami ar Modibbo Adama dake yola tace daman abunda suke gudu kenan na kada gwaknati ta kara kudin makaranta amma sai aka kasa fahintarsu harma da zargin cewa suna wannan fafutuka ne domin Kansu. Shugaban kungiyar Malamain Jami o i na Jami ar Kodibbo Adama Dr El Maude Jibril Gambo na ya bayana haka a zantawarsa da Jaridar Al Nur a yola. Dr El Maude yace sukam karin kudin baizo musu da mamakiba saboda daman suna fadawa mutane musammanma iyaye da su maramusu baya a kokari da sukeyi na ganin an inganta Jami o in kasan nan amma suka ki wasuma suka shiga zarkinsu da lalata bangaren ilimi. Dr Jibril yace yanzu kam yar manuniya ta nuna cewa ashe abunda kungiyar keyi yana kan hanya saboda haka ya kamata suyi karatun ta nutsu sukarayi gwamnati da ta rage kudin makarantar saboda yaran talakawa su samu suyi karatu yadda ya kamata. Yace ko shakka babu hwaknati tana iya daukan nauyin kakarantu ba tare da Karin kudin makarantarba in aka dubi yadda ake zargin wasu Jami an gwamnati da wawure kudaden jama a. Don haka ya kamata gwamnatin ta janye Karin kudin makaranta domin zaiyi sanadiyar wasu zasu iya barin karatun a Jami o i dake fadin kasan nan. A kashe dai ya kirayi iyaye dama daluben da su baiwa kungiyar hadin kai da goyon baya domin ganin kungiyar ta ASUU ta cimma burinta na ganin an inganta Jami o i gwamnati dake fadin kasan nan.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.