Kungiyar Attarahum Faundation ta kaddamar da sabbin suwagabanninta nq kananan hukumomi.

Kungiyar Attarahum Faundation dake jahar Adamawa ta kaddamar da shuwagabaninta na kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar Adamawa. An dai gudanar da taron kaddamawan ne a yola ta kudu a jahar Adamawa, wanda ya samu halartan Al umma dama da suka hada da yan siyasa da dai sauransu. Da yake jawabin maraba shugaban gidauniyar ta Attarahum Foundation a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ya baiyana dalilinsu na kafa wannan gidauniya domin taimakon kai da kai harma da taimakawa marassa galihu, marassa lafiya,marayu, gajiyayyu da dai sauransu. Wanda kuma hakan yasa suka ga ya dace su fadada gidauniyar zuwa kananan hukumomi wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cimma burinsu na taimakawa al umma baki daya. Don haka nema ya kirayi al umma da sukasance masu kafa irin wannan gidauniyar domin taimakawa jama a tare da shawartan masu hanu da shuni da suma su bada tasu gudumawa wajen tallafawa jama a. Malam muktar Dayyib ya yabawa yar takaran gwamnat karkashin jam iyar A P C a jahar Adamawa sanata Aishatu Dahiru Binani bisa goyon baya da kuma hadin kai da take baiwa gidauniyar. Shima a jawabinsa sakataren gidauniyar a jahar Adamawa sheik Mamman Nasir yace tun daga kafa gidauniyar kawo yanzu sun gudanar da taimako wa al umma daban daban tun daga matsalolin korona harma na cutar amai da gudawa harma da kayakin karatu ga dalube daban daban. Ya kuma shaidawa shuwagabannin gidauniyar a kananan hukumomi cewa irin wadannan taimako sa sucigaba dayiwa al umman yankunansu da suka hada da musulmai dama mabiya addini kirista Wanda hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya. Sanata Abdul Aziz Nyako wanda Muhammed Hassan Turaki ya wakilta a wurin taron ya yabawa gidauniyar bisa na mijin kokari da sukeyi waken taimakawa al umma ya kuma kirayi shuwagabanni da aka kaddamar da sukasance masu sadaukar da kansu wajen taimakawa jama a. Shima AbdulRazak Namdas wanda Usman Ibrahim ya wakilta ya nuna jin dainsa dangane da yadda wannan gidauniyar ke gudanar da aiyukansa kuma yayi fatan ganin irin wannan taimako zai zama sillan cigaban gidauniyar baki daya. Itama da take nata jawabi sanata Aishatu Dahiru binani wanda Bala Jingi ya wakilat ta nuna goyon bayanta ga wannan gidauniyar don haka nema ta taimaka da wurinda aka gudanar da taron. Tare da shawartan shuwagabanin da sucigaba da irin wannan taimako da sukeyi. Da yake jawabi a madadin suwagabannin kananan hukumomon shuhaban karamar hukumar Mubi ta arewa Abubakar Bala Dauda ya godewa yayi bisa wannan shugabanci da aka basu tare da tabbatar dacewa zasuyi dukkanin abunda suka dace domin taimakawa al umma domin cigaban gidauniyar a fadin kasan nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE