Kungiyar yan kasuwa na arewa sun goyi bayan Tinubu da Shetima.

Kungiyara yan kasuwar arewacin Najeriya masu rajin goyon bayan Bola Ahmed Tinubu da Shetima a neman takaran shugaban kasa kakashin Jam iyar A P C a Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Ko odinatan kungiyar ta kasa Alhaji Adam Hassan Ibrahim ne ya baiyana haka a zantawarsa da Jaridar Al Nur ta waya inda yace dalilinsu na goyon bayan Tunibu da Shetima saboda Bola Tinubu ya gaji kasuwanci saboda haka in har ya samu nasara to yan kasuwa zasu samu tamogashi a fafin Najeriya.
Alhaji Adam Hassan yace Tinubu ya gudanar da aiyukan cigaban a jaharsa wato Lagos a lokacin yana gwamna ya kuma taimakawa mutane da dama a sassa daban daban dake fadin kasan nan baki daya, don haka nema suka ga ya dace su marawa Tunibun baya domin ya kai ga samun nasara a zaben shekara ta 2023. Alhaji Hassan suna da yakinin cewa idan Bola Tunibu ya samu nasara zai maida hankali wajen bunkasa kasuwanci dama bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma uwa uba matsalar tsaro harma da samatwa matasa aikinyi ta hanyar koyardasu sana o i daban daban. Hassan Ibrahim yace kasancewarsu yan arewa kuma suke goyon bayan Tunibu saboda irin aiyukan cigaba da sukaga yayiwa jaharsa ta Lagos dama yadda ya tallawa wasu wadanda suma sun tsaya da kafarsu shiyasa suka ga ya cancaci su mara masa baya domin a cewarsa in har ya samu nasara zai takarawan gaske wajn kawo karshen dukkanin kalu balen rayuwa da ake ciki. Kuma zai cigaba da aiyukan cigaban wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi. Saboda haka nema ya shawaci yan Najeriya musammanma yan kasuwa da su marawa Tinubun baya domin shine wanda zai sharea yan kasuwan hawayensu. Ya kuma yi fatan za a gudanar da zabe shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya ba tare da wata matsalaba don haka nema yake shawartan yan Najeriya da su kasance masu yin adu o i akoda yaushe da kuma hada Kansu da kuma nunawa juna kauna domin samar da zaman lafiya dama cigaban kasàn nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE