Kungiyar yan sa kai ta karrama membobinta a jahar Taraba.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Domin ganin ta inganta aiyukan jami anta kungiyar yan sa kai da aka fi sani vigilante ta shirya liyafa da baiwa kautar yabo wa wasu daga cikin yan kungiyar.
Bikin liyafar da bada kautar yabonne a Jalingo fadar gwamanatin jahar Taraba inda yan kunguyar da yawansu ya kai dari da hamsin 150 suka karbi kautar yabon biyo bayan yanda suka sadaukar da kansu wajen gudanar da aiyukansu.
Kwamandan kungiyar a jahar Taraba Bello Arabi da yake jawabi a wurin taron ya kirayi wadanda aka karramar da suci gaba da irin wannan na mijin kokari da sukeyi wajen kare al ummarsu.
Kwamandan wanda mataimakinsa DCV Dominic Kabanya ya wakilta ya kirayi membobin kungiyar da su cigaba da baiwa hukumomin tsaro hadin kai domin kare rayuka dama dukiyoyin al ummah. a fadin jahar.
Bello Arabi ya kirayi gwamnatin jahar Taraba dama kungiyoyi irinsu hukumar raya yankin arewa masau gabas NEDC da sauransu da aukasance suna taimakawa kungiyar tasu da kayakin aiki kamar motoci wanda hakan zaikara musu kwarin gwiwa cigaba da aiyukansu yadda ya kamata.
Kwamandan yace sun taka rawan ganin a cikin shekara ta 2022 ta wajen tsare masu aikata laifuka a tsakanin al ummah tare da yin alkawarin kara kaimi cigaba da aiyukansu.
Shima mataimakain kwamandan ACV Shadrach G Shadrach ya gargadi membobin kungiyar da su nisanta kansu daga karban cin hanci da rashawa a duk lokacin da suke gudanar da aiyukansu.
Da yake nashi jawabi mai hulda da jama a a kungiyar ACV Suleiman Aliyu kaf a yankin arewa masau gabas jahar Tarabace koma baya in aka kwatanta da makabtansu wadanda gwamatoci jihohinsu su taimaka musu da motoci don haka nema yake kira ga gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku ya dubi Lamarin domin ya taimaka musu.
Comments
Post a Comment