Kungiyoyi dari biyar ne suka kudiri aniyar ganin Alhaji Atiku Abubakar yayi nasara a zabe mai zuwa.

A kalla kungiyoyi Nagoya bayan Atiku dari biyar ne sukayi rijista domin ganin Alhaji Atiku Abubakar yayi nasara a Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Ko odinatan Atiku Mandate na kasa Alhaji Sa idu Komsari ne ya baiyana haka a wajen taron shuwagabain kungiyoyin da aka gudanar a yola. A taron dai kungiyoyin sunyi Alwashin ganin dan takaran shugaban kasa a jam iya P D P Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a zabe mai zuwa. Kungiyoyin dai sun hada Kansu tare da nuna jindadinsu da shirya wannan taro Wanda hakan ya nuna cewa wazirin Adamawa zai kai ga samun nasara. Don haka Alhaji Sa idu Komsiri ya kirayi kungiyoyin da su tabbata sunyi aiki kafada da kafada da sauran kunyoyin domin ganin an samu nasara a Babban zaben. Ya kuma kirayin yan Najeriya da su hada kai su baiwa Alhaji Atiku Kuri u wanda hakan zai taimaka ya samu damar lashe zaben sjekara ta 2023. An dai gudanar da jawabai daban daban a wurin taron inda suwagabanin kungiyoyin suka baiyana manufofinsu na goyon bayan Alhaji Atiku da kuma irin shiri da sukeyi na bashi kuri u a lunguna lunguna dama sako sako.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE