Mazauna yankin gwalamba sun kirayi gwamnatoci a dukkanin matake domin gyara musu hanya.

Mazauna yankin Gwalnba dake gundumar Lamtari a cikin karamar hukumar yola ta kudu sun krayi gwamnatin tarayya dana jahar harka dana kananan hukumar da su taimaka musu da gyara musu hanya, wutan lantarki cibiyar kiwon lafiya da dai sauran kayakin more rayuwa. Hardon gwalamba kuma mataimakin shugaba kungiya Pulaku Jamde Jam Foundation a jahar Adamawa Hassan Ali Soje ne yayi wannan kira a zantawarsa da Jarida Al Nur a yola. Hassan Ali Soja yace kiran gwamnatocin ya zama wajibi duba da irin yanayi da suke ciki na raahin hanya musammanma idan ake a damina yayi wanda da gomin goshi suke shiga da fita anguwar tasu ga kuma matsalar wutan lantarki wanda haka yayi sanafiya koma baya sosai a cikin unguwar tasu. A cewar Ali Soja da in har aka gyara musu hanya zasu samu damar bunkasa harkokin kasuwancin yankin kuma gwamatin zata samu kudin shiga. Saboda haka ya kamata gwamnatocin suyi dukkanin abinda suka dace domin suma su samu walwala yadda ya kamata. Ya kara da cewa Babban matsalarma itace da zaran an samu matsalar rashin lafiya tofa tashin hankali ya samesu saboda rashin kyau hanya ya na basu wahalar gaske kafin sukai ga asibiti mafi kusa dasu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE