Mutane hudu ne suka mutu a wani hatsrin jirgi mai saukar angulu a Australia.
Akalla mutane hudu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon tsarin da wasu jirage masu saukan angulu sukayi a kusa da teku dake Australia.
Jami an yansandan yankin da lamarin yaru sunce hatsrin ya farune alokacin da daya jirgin kekokarin tashi daya kuma yana sauka.
Wadanda suka mutundai suna cikin jirgi dayane a yayinda sauran ukun kuma suna jinya cikin wani yanayi maiwahala.
Cikin wadanda suka mutun dai biyu yan kasan ingilane karamar yadda mai magana da yawun ma aikatar kasashen wajen Australia ya baiyanawa manema labarai.
Mutane biyar cikin shida wanda ke cikin daya jirgin da sukayi saukan gaggawa sun samu raunuka.
Fira ministan kasa ta Australia Anthony Albanese yace kasar ta kadu kwarai da jin labarin aukuwar lamarin.
Yace zasu dauki dukkanin matake da suka dace domin kula da wadanda suka jikkata sakamakon tsarin.
Comments
Post a Comment