Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kimtsa tsaf domin taran shugabann kasa Muhammadu Buhari.

A kokarinta na inganta tsaro da kuma dakile aiyukan ta addanci rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin daukan dukkanin mataken da suka dace domin ziyaran da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola wanda aka rabawa manema labarai a yola. A sanarwan dai anjiyo kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Sikiru Kayode Akande na cewa dukkanin shirye shirye ya kammala domin taran shugaban kasa do haka rundunan da sauran hukumomon tsaro sun hada kai domin ganin ba a samu matsalaba kafin dama bayan ziyaran shugaban kasa. Kwamishin yace za a takaita zirga zirgan ababen hawa a wuraren da shugaban kasa zaibi don haka al umma su kasance masu bin doka.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE