Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wasu matasa shida da ake zargin yan shilane

Akokarinta na dakile aikata laifuka a fadin jahar rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cika hanu da wasu matasa yan shila guda shida wadanda suka addabi anguwar luggere kuma sun kware wajen balla shaguna da shiga gidaje. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Sanarwan ta cigaba da cewa biyo bayan da Jami an ta ke sintiri domin ganin ba asamu matsalaba a lokaci dama bayan ziyaran da shugaban kasa muhammadu Buhari zai kawo jahar Adamawa,Wanda hakan ya kai ga basu sa a kama wadanda ake zargin. A sanarwan anjiyo kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Sikiru Kayode Akande ya yabawa Jami an yan sandan bisa na mijin kokari da sukayi wajen kama wadanda ake zargin. Kwamishin yan sandan ya kuma kirayi al umma dake fadain jahar da sukasance masu taimakawa rundunan yan sandan da wasu bayanai da zaibawa Jami an yan sandan damar kama masu aikata laifuka a tsakanin al umma. Ya kuma tabbatarwa gwamnatin jahar dama al umma jahar cewa rundunan yan sandan a shirye take wajen kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya. Kawo yan zu dai rundunan ta gano kwanfitoci sha hudu dama wasu kayaki a wurin wadanda ake zargin.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE