Rundunan yan sandan jahar Adamawa tasha alwashin ganin an gudanar zaben 2023 lafiya,
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin ganin an gudanar da Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku cikin kwanciyar hankali ba tare daatsaloliba.
Rundunan ta baiyana haka ne a wata sanarwa da kakakin rundunan yan sandan na jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya sanyawa hanu wanda aka rabawa manema labarai a yola.
Rundunan tace ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a samu tashin hankaliba a lokaci dama bayan zaben.wanda kuma daukan matakin hakan ya biyo bayan tattaunawa da kwishinan yan sandan jahar Adamawa Sikiru Kayode Akande yayi da dukkanin masu ruwa da tsaki dangane da tsaro domin ganin ba a samu matsalaba a lokacin zabe.
Kwamishinan ya kuma shawarci sauran hukumomin tsaro da suyi aiki kafada da kafada domin ganin an samu nasaran gudanar da Babban zaben. Tare da kiran Jami an tsaro da sukasance masu sanya ido sosai domin kama duk wanda yayiwa doka karan tsaye.
Kwamishinan ya kuma tabbatarwa al umma jahar cewa jami ansu a shirya suke su kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya. Don haka akwai bukatan jama a su baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya a lokaci dama bayan Babban zaben.
Comments
Post a Comment