Rundunan yan sandan jahar zamfara ta kama wadanda ake zargi da kaiwa yan bindiga makamai.

A kokarinta na dakile aiyukan ta addanci a jahar Zamfara rundunan yan sandan jahar tayi nasaran kama wasu mutane biyu da ake zargi da safaran makamai wa yan bidigan a jahar ta zamfara. Kakakin rundunan yan sandan jahar Zamfara SP Muhammed Shehu ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Gusau fadar gwamnatin jahar Zamfara. Sanarwan tace an samu nasaran cafke mutanenne akan hanyar Gusau Wanke Dansadau tare da albarushe har 325 da kuma binga kiran Ak 47 Wanda ake zargin dai sune Emmanuel Emmanuel ta da abokiyar aikinsa wato Nana Ibrahim. A cikin sanarwa an jiyo kwamishinan yan sandan jahar CP Kolo Yusuf ya tabbatarwa al umma jahar cewa rundunan a shirye take takare rayuka dama dukiyoyin al umma dake fadin jahar baki daya. Don haka nema ya ke kira ga daukacin al umma jahar da sukasance masu taimakawa rundunan da wasu bayanain sirri da zai baiwa rundunan yan sandan damar cika burinta na inganta tsaro a fadin jahar Zamfara baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE