Zaben shekara ta 2023 an kirayi al ummah musulmai da suje su karbi katin zabensu.

Daga Sani Yarima Jalingo. Ganin cewa zaben shekara ta 2023 nata karatowa, an kara yin kira ga Al'umma dasu fita zuwa karban katinan zaben su a ofishoshin hukumar zabe ta kasa dake jahohin su. Wani Malamin Addinin Musulunci dake garin Mutum Biyu a karamar hukumar Gassol ta Jihar Taraba, Ustaz Sani Yusuf Darul-Hadith yayi wannan kiran alokacin da yake zantawa da wakilin mu dake Jalingo ta wayan hannu. Ustaz Sani Yusuf Darul-Hadith Mutum Biyu wanda muka zanta dashi ta wayan hannu jimkadan bayan an idar da sallan Juma'an data gabata yace nasihan da yayiwa al'umman musulmi a Babban masallacin kofar fadan mai Martaba Sarkin Mutum Biyu, Alh. Muhammadu Sani Duna shine na cewa karban katinan zaben su ya zama wajibi domin zai basu daman zaben 'yan takaran da suke da kyakkyawan zato a kansu. Ustaz Sani Yusuf Darul-Hadith Mutum Biyu ya kuma kara jawo hankalin matasa da karsu yarda arinka amfani dasu a matsayin 'yan barandan siyasa. A karshe, Malamin Addinin Musulunci, Ustaz Sani Yusuf Darul-Hadith yayi wa garin na Mutum Biyu, Jihar Taraba, Najeriya dama duniya baki daya fatan samun zaman lafiya dawwa mamme.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE