Zaben shekara ta 2023 kungiyar Atiku mandate tasha Alwashin gani Atiku ya samu nasara a zaben mai zuwa.

Kungiyar Atiku Mandate ta sha Alwashin ganin Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a Babban Zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Ko odinatan kungiyar ta kasa Alhaji Sa idu komsari ne ya baiyana haka a zantawarsa da Jaridar All Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Sa idu yace akwai tsare tsrea da dama da kuma matake masu yawa da sukayi wanda hakan zai taimaka wajen samun nasaran Alhaji Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa wanda za ayi a shekara ta 2023. Alhaji Komsari ya kirayi daukacin yan Najeriya musammanma yan arewa da su sanifa wannan damace a garesu da su zabi Atiku wanda zai ceto kasan nan daga cikin matsaloli da ake fuskanta da suka hada da tattalin arziki, tsaro, da dai saraunsu. Ya kuma baiyana cewa wazirin wato Atiku Abubakar yana da kwarewa a fannoni daban daban kuma ya goge a fanin mulki da kasuwanci don haka akwai buiatan yan Najeriya su bashi hadin kai da goyon baya domin ganin ya samu nasara lashe zaben shugaban kasa a zabe mai zuwa. Ya kara da cewa Kungiyar Atiku mandate ta kimtsa tsaf domin ganin Atiku ya kai ga samun nasara ta kirayi yan arewa masau gabas da kada su bari wannan damar da kuskure musu. Alhaji Sa idu yayi fatan Allah yasa a kammala zabe cikin kwanciyar hankali ba tare d matsaloliba, don haka nema ya shawarci yan Najeriya da su cigaba da yin au o I domin samar da zaman lafiya a fadin kasan nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE