Akalla yaran mata dari ne dai suka samu horo kan sana o i dogaro da kai a sansanin yan gudun hijira a jahar Adamawa.

A yayinda ake gudanar da bikin ranan yaran mata ta duniyar a wannan shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Hakan yasa kungiyar Action Health tare da hadin gwaiwar kungiyar raya kasa ta Amurka USAID da kuma Asusun Al umma na majalisar dinkin duniya UNFPA sun horar da yaran mata sana o i daban daban a sansanin yan gudun hijira dake Daware a cikin karamar hukumar Fufore a jahar Adamawa. Bikin na bana mai taken inganta rayuwar yaran mata domin samar da shugabanci da ya dace. Da kuma samarwa yaran mata yancinsu yadda ya kamata. Da yake jawabi dangane da ranan yaran matan ta duniya shugaban sansanin yan gudun hijiran Umar Bappa ya yabawa kungiyoyin bisa wannan taimako da sukayi musu inda yace al ummarsu zasu samu cigaba harma da inganta rayuwarsu.
Ardon Daware Umaru Bobbo wanda Ezra Christopher ya wakilta shima yabawa yayiwa Action Health tare da takwarorinsu bisa wannan na mijin kokari da sukayi na tallafawa yan gudun hijira wanda hakan zai basu damar dogoro da Kansu ba tare da dogara da wasuba. Suma yaran matan musammanma wadanda suka amfana da taimakon sun baiyana farin cikinsu tare da godewa kungiyoyin bisa wannan taimako da sukayi musu, wanda acewarsu hakan zai basu damar gina rayuwarsu yadda ya kamata. Cikin sana o i da aka koyawa yaran matan dai sun hada da tela da dai saraunsu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.