An baiyana cewa nasaran da gwamna Fintiri yayi a kotu nasarace ga Al ummar jahar Adamawa.
Usman Abubakar wanda akafi sani da Manu Ngurore yana Mai taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murna yin nasara a kotu sauraro koke koken zaben gwamna a zamanta na anan Yola.
Alhaji Usman Abubakar Wanda shine mataimaki na musamman akan harkokin noma da sana o I na gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa..
Alhaji Usman yace wannan nasara da gwamna yayi ya nuna cewa Yan jahar Adamawa basuyi zaben tumun dareba domin kuwa an basu abinda suka zaba kasancewa gwamna Yana gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Alhaji Usman yace ba Wanda ya dace ya Mulki jahar kamar Ahmadu Umaru Fintiri saboda yadda ya gunara da aiyuka daban daban harma da bada Ilimi kyauta wa Al ummar jahar tare da bunkasa bangarori daban daban da suka hada da Noma, kiwon lafiya, koyawa matasa da mata sana o I daban daban domin dogaro da kansu.
Ya Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sucigaba da baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran cigaba da gudanar da aiyukan cigaba da yake yiwa Al ummar jahar Adamawa.
Alhaji Abubaka ya yi Adu ar Allah madaukakin sarkin ya baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri nasara a dukkanin aiyukan da yasa a gaba. Ya Kuma kareshi a duk inda yake.
Comments
Post a Comment